Rundunar sojin Nijeriya, ta musanta harbin masu zanga-zanga a Lekki Toll Gate da ke Legas, inda ta ce gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ne ya kira su domin zuwa wajen masu zanga-zanar #ENDSARS.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun runduna ta 81 ta sojin da ke Legas Manjo Osoba Olaniyi ya fitar, ta ce rundunar sojin Nijeriya ta 81 ta ga wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, wanda ya ke nuna cewa sojoji sun kashe farar hula da ke zanga-zanga a Lekki.

Ya ce wannan zargin ba gaskiya ba ne, kuma hakan na so ya janyo rashin zama lafiya ne kawai a cikin ƙasa, ya na mai cewa, gwamnan jihar ne ya yanke shawarar kiran sojoji domin kawo ƙarshen rikicin da ke faruwa. Sanarwar sojojin ta na zuwa ne kwanaki bakwai bayan abin da ya faru a Lekki, inda bayan nan ne aka fara samun rikice-rikice da su ka haɗa da fasa rumbunan abinci a wasu jihohin Nijeriya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *