Shugabar Hukumar kula da ingancin magunguna da abinci NAFDAC, Mojisola Adeyeye, ta fallasa yadda ta gaji tulin bashin naira biliyan 2 da miliyan 300 a hukumar.

Ta ce ta karbi ragamar shugabancin hukumar a lokacin da motocin hukumar kalilan ne ke aiki.

Mojisola ta bayyana haka ne, yayin da ta ke jawabi wajen kare kasafin hukumar na shekara ta 2021 a gaban Kwamitin Lafiya na Majalisar wakilai.

Ta ce ta karbi shugabancin hukumar cike da muradin inganta ta yadda za ta iya rike kan ta, amma dimbin basussukan da ta iske ana bin hukumar da kuma yadda kayan aiki su ka yi karanci sun kashe mata gwiwa.

Mojisola ta kara da cewa, ya zuwa watan Yuni, hukumar ta tara naira biliyan hudu daga kudaden da ta ke saida fom da haraji, da tara da kudaden da masana’antu ke biya a matsayin haraji har zuwa watan Yuni.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *