Shugaba Muhammadu Buhari, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya su guji kalamai tare da aikata abubuwan da za su janyo cikas ga hadin kai da kuma ci-gaban kasar nan.

A cikin wata sanarwar da Fadar Shugaban kasa ta fitar, Buhari ya bayyana muhimmancin haɗin kan ƙasa, wanda ya ce da tsada aka same shi.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne, yayin bikin kaddamar da alamar tunawa da mazan jiya da kuma gidauniyar naira miliyan 10 ga kungiyar tsofaffin sojojin.

Buhari ya jaddada cewa, karfin Nijeriya ya dogara ne a kan bambance-bambancen ta, sannan ya yi jinjina wa sojoji maza da mata da ke aikin tabbatar da tsaro wajen yaƙi da Boko Haram da ‘yan bindiga a sassan ƙasar nan.

Shugaba Buhari ya kuma karrama sojojin da su ka kwanta dama, waɗanda ya ce sun sadaukar da rayukan su a lokacin yaƙin duniya da yaƙin basasa da kuma ayyukan tabbatar da zaman lafiya a ƙasashen duniya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *