Ministar Ma’aikatar Jin-kai da Ci-gaban Al’umma Sadiyya Umar Farouk, ta kare kan ta a kan batun kayan tallafi da ta ce ta raba wa jihohi domin raba wa al’umma.

Sadiyya Farouk ta shaida wa manema labarai cewa, ta sauke nauyin da aka dora mata bayan zargin ta da aka rika yi a kan kayan tallafi kafin wawason da wasu su ka yi a rumbunan ajiye kayan abinci.

Ta ce sun ba gwamnonin jihohi umarnin rarraba kayan tun a lokacin da su ka kai musu, don haka ta ce sun sauke nauyin da shugaban kasa ya dora masu na ba jihohi kayan tallafin.

Sai dai ƙungiyar gwamnonin Nijeriya ta ce, kayan da aka sace ba na gwamnati ba ne, tallafin da ‘yan kasuwa su ka bada ne.

Yayin wata ziyarar aiki da ta ke yi a Jihar Zamfara, ministar ta ce da ma ta san gaskiya za ta yi halin ta, domin ta san ta na aiki ne tsakani da Allah don ta sauke amanar da aka ɗora mata.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *