Shugaban rundunar sojin kasa ta Nijeriya Janar Tukur Yusuf Buratai, ya umarci manyan sojojin kasa su bayyana kadarorin da su ka mallaka.

Wannan dai ya na cikin dokar kotun kula da da’ar ma’aikata, ta yadda jami’an gwamnati da sauran ma’aikatu za su yi gaskiya.

Da ya ke jawabi a wajen wani taro, Janar Buratai ya ce yin hakan zai tabbatar da aiki da gaskiya da kuma yin abin da ya dace a aikin su.

Shugaban hukumar kula da da’ar ma’aikata Isa Mohammed, ya yi wa sojojin kasa jawabi a wajen taron ta bakin Farfesa Samuel Ogundare da ya wakilce shi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *