Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci matasan Nijeriya su yi amfani da damar da aka ba su a shirye-shiryen da gwamnatin sa ta fito da su don rage fatara da rashin aikin yi.

Ana dai gudanar da Shirye-shiryen ne a karkashin Ma’aikatar Harkokin Jin-kai da Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya domin a kyautata rayuwar matasa da sauran mabukata.

Buhari ya bayyana haka ne a cikin jawabin da ya gabatar a  kan tarzomar ‘EndSARS, inda ya ce duk da raguwar rashin kudin shiga da Nijeriya ke fama da shi da kuma tarnakin da annobar korona ta kakaba mata, Gwamnatin Tarayya ta fito da tsare-tsaren da ke taimaka wa masu kananan sana’o’i da matasa da fakirai ta yadda za a taimaki rayuwar su.

Ya ce, gwamnati ta fito da hanyoyi da tsare-tsare na musamman, domin matasa da mata da kuma mutanen da ke fama da babu a cikin al’umma.

Shirye-shiryen kuwa sun hada da shirin ceto ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga ƙangin fatara nan da shekaru 10, da kuma shirin naira biliyan 75 na Asusun Gina Matasa na Kasa, inda za a samar da damarmaki ga matasa da kanana da tsaka-tsakin sana’o’i.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *