Rundunar ‘yan sandan Nijeriya, ta ce an kashe jami’an ta shida tare da raunata 38 sakamakon barkewar rikici a zanga-zangar nuna adawa da cin zalin ‘yan sanda a jihar Legas.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Legas Hakeem Odumosu ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai, inda ya ce jami’an da aka kashe sun hada da Yard Edward da Olayinka Erinfolami, da Adegbenro Aderibigbe da Abejide Abiodun da wasu karin mutane biyu.

An dai samu mummunan tashin hankali a jihar ta Legas, bayan bata-gari sun mamaye jihar su na kone-kone da lalata gine-ginen gwamnati, lamarin da ya janyo kafa dokar hana fita ta tsawon kwanaki.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *