Runduna ta musamman dake yaki da ayyukan ta’addanci da ake yiwa lakabi da Operation Sahel Sanity, ta kasha ‘yan ta’adda 38 tare da kama wasu 93 a yankin arewa maso yammacin Najeriya a tsakanin 4 ga watan Satumba zuwa 25 ga wannan watan.

Babban jimi’in yada labarai da hulda da jama’a na rundunar Brigadier Janar Bernard Onyeuko, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Faskari dake jihar.

Ya ce mutanen 93 da aka kama sune suke kaiwa ‘yan ta’addan kayayyakin amfanin yau da kullum.

Onyeuko, ya ce jami’an tsaron sun kwato wasu muggan makamai da karin wasu kayayyaki da dama.

Ya ce baya ga makaman rundunar ta kwato shanu 131 da tumakai da raguna 154, sai rakumi guda daya, sannan ta kubutar da wasu mutane da suka yi garkuwa dasu su 108.

A karshe ya yabawa al’ummomi da irin sahisan bayanai da suka bada da ya ba jami’an tsaron kwarin gwiwar kai samamen a maboyar ‘yan ta’addan. 

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *