Gwamnatin tarayya ta ce akwai fargabar sake bullar cutar korona a Najeriya sakamakon cunkoso da saba dokokin kariya da aka yi a lokacin zanga-zangar adawa da rundunar SARS.

Shugaban kwamitin yaki da cutar na gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya bayyana haka a lokacin da yake magana wajen taron da kwamitin ke shiryawa a Abuja.

Mustapha wanda shine sakataren gwamnatin tarayya ya ce annobar cutar ta korona na sake karuwa a kasashen duniya, wanda yanzu haka wadanda suka kamu sun haura milliyan 43.

Sannan ya yabawa hadakar kungiyoyi dake yaki da cutar ta korona ta hanyar wayar da kai, bisa hada hannu da tayi da jihohi tare da raba kayayyakin tallafi ga al’umma.

Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya su zama masu bin doka da oda, tare da ba hukumomin tsaro hadin kai domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban kasa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *