Kamfanin matatar man fetur na Najeriya NNPC ta bukaci masu ababen hawa da kada su shiga wata fargabar karancin man fetur a wasu sassan Najeriya.

Babban jami’in kula da sashen yada labarai da hulda da jama’a Kennie Obateru, ya bayyana haka a Abuja.

Ya ce layin man fetur da ake samu na zuwa ne sakamakon dokar takaita zirga-zirga da aka sa a wasu jihohi biyo bayan zanga-zangar adawa da rundunar SARS.

Ya ce dokar ta shafi zirga-zirgar manyan motoci dake dakon man zuwa sassa daban-daban na Najeriya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *