Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta ce za ta fara bincike kan kayayyakin tallafi da aka sace.

Hukumar ta bayyana hakan ne a shafinta na yanar gizo, ta ce ya zama wajibi ta gudanar da binciken sakamakon irin kayayyakin da aka gano a lokacin zanga-zanga.

Wannan na zuwa ne bayan wasu ‘yan Najeriya da dama sun bukaci hukumar ta ICPC ta gudanar da cikakken bincike tare da gano dalilan da suka sa aka boye kayayyakin ba tare da rabawa al’umma ba.

Hukumar ta ce za a ta gudanar da binciken ne a hukumomin da suke da alhakin samarwa tare da rarraba kayayyakin tallafin da aka samar domin rage radadin cutar korona.

Sannan ta ba ‘yan Najeriya tabbacin cewa da zarar ta kammala bincike, za ta sanar da sakamakon da ta gano, sannan za a hukunta duk wadanda aka samu da laifi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *