Majalisar tattalin arziki ta Najeriya ta kafa kwamitin na musamman da zai tattauna da matasa da masu ruwa da tsaki da zai yi aiki tare da magance rikice-rikicen da aka samu a zanga-zangar adawa da SARS.

Mai taimakawa mataimakin shugaban kasa kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Laulu Akande, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.

A statement by the Senior Special Assistant to the President on Media and Publicity, Laolu Akande, said the committee is headed by Osinbajo.

Majalisar ta dauki wannan mataki ne a taron mako-mako da take gudanarwa wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta a Abuja.

Mataimakin shugaban kasan wanda shi zai jagoranci tawagar ya ce kwamitin zai gudanar da bincike tare da fito da wasu sabbin tsare-tsare da za su kare faruwar haka a nan gaba.

Wadanda suka halarci taron sun nuna goyon bayansu ga matakin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka, na umurtan hukumomin tsaro su magance matsalolin da suka dabaibaye zanga-zangar da aka gudanar a wasu jihohi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *