Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka ana ciyar da yara dubu dari 2 da 82 da dari 5 da 29 a karkashin shirin ciyar da dalibai a jihar Zamfara.

Ministan kula da harkokin jin kai da walwalar jama’a Sadiya Umar Farouq ta bayyana haka a wajen taron jin ra’ayoyin jama’a da ya gudana a Gusau babban birnin jihar.

Ta ce ana gudanar shirin ne a makarantu dubu 1 da dari 7 da 59 dake kananan hukumomi 14 a dake fadin jihar.

Ministar ta kara da cewa gwamnati ta dauki ma’aikata masu dafa abinci dubu 2 a jihar da suke samar da abincin ga daliban lokaci zuwa lokaci.

Sadiya ta yabawa jihar Zamfara bisa matakin da ta dauka na farfado da tattalin arziki, sannan ta bada tabbacin cewa ma’aikatar ta za ta ci gaba da hada hannu da jihar wajen kaddamar da wasu ayyuka da suka shafi inganta rayuwar al’umma.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *