Gwamnatin jihar Kano ta ce ta ware kaso na musamman a kasafin kudin jihar domin biyan bukatun mutane masu bukata ta musamman dake fadin jihar.

Daraktan tsare-tsare na ma’aikatar kasafi da tsare-tsare na jihar Muntari Yakasai, ya bayyana haka a lokacin da shugaban kungiyar masu bukata ta musamman Shaga Musa, ya kai masa ziyara a Kano.

Ya ce an sanya kasafin kudin ne a karkashin ma’aikatar kula da walwalar mata da ci gaban kasa.

Yakasai ya ce gwamnatin jihar ta dauki wannan matakin ne biyo bayan bukatar da kungiyar ta gabatarwa gwamnatin jihar, wanda bayan tattaunawa gwamnatin ta ga akwai bukatar daukar matakin hakan.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *