Zababen gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki da mataimakin sa Philip Shu’aibu sun kai wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyara a fadar shugaban kasan dake nan Abuja.

Wannan itace ziyara ta farko da Gwamna Obaseki, ya kai wa shugaban kasa bayan zarcewar sa kan mulki karo na biyu.

Gwamna Obaseki da mataimakin sa da wasu ‘yan majalisar tarayya sun ce sun kai ziyarar ne don yi wa shugaban kasa godiya

Obaseki ya lashe zaben sa na farko ne a karkashin jam’iyyar APC, amma daga bisani ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP, inda ya sake lashe zaben karo na biyu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *