Uwar jam’iyyar APC ta yi watsi da dakatarwar da wani ɓangare na Jam’iyyar a jihar Ekiti ya yi wa gwamnan jihar kuma shugaban gwamnonin jam’iyyar Kayode Fayemi.

Sanarwar da Uwar jam’iyyar ta APC ta bayar ta ce babu wata sanarwa a hukumance da ta samu daga ɓangaren jam’iyyar a Ekiti kan dakatar da Kayode Fayemi da kuma wasu mambobin jam’iyyar.

Kwamitin zartarwa na Jam’iyyar APC reshen jihar Ekiti ya dakatar da gwamnan jihar Kayode Fayemi daga jam’iyyar inda sanarwar ta ce an dakatar da Gwamna Kayode ne sakamakon zargin yin abubuwan da suka saɓa wa jam’iyyar da suka haɗa da ungulu da kan zabo.

Kafar talabijin ta Channels ta ruwaito sanarwar na cewa Mista Fayemi ya saɓawa dokokin jam’iyyar bayan zargin sa da taka rawa a zaben jihar Edo.

Kuma an zargi gwamna Fayemi da karɓar baƙuncin fitaccen ɗan Jam’iyyar PDP babbn mai adawa da Buhari Femi Fani-Kayode a lokacin zaɓen Edo.

A martanin ta, uwar jam’iyyar ta ce har yanzu gwamna Kayode Fayemi ne uban jam’iyyar a jihar Ekiti ne.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *