Wasu ‘yan ta’adda daga cikin wadanda ke zanga-zangar adawa da rundunar Sars, sun lalata ofishin hukumar kiyaye aukuwan haddura na kasa reshen jihar Legas, inda suka bankawa motoci da dama wuta.

Kwamandan hukumar dake kula da shiyyar Olusegun Ogungbemide, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan aukuwar lamarin a Legas.

Ya ce bayan cinnawa motocin wuta da lalata wasu kayayyaki da dama, rundunar ‘yan sanda ta kai dauki inda ta shawo kan matsalar, sai dai matasan sun sake komawa harabar wajen a lokacin da jami’an ‘yan sandan suka tafi.

Ogungbemide, ya ce bai kamata ace matasan sun yiwa ofishin hukumar haka ba, duba da yadda take kokari wajen tsare rayukan ‘yan Najeriya dake tafiye-tafiye a hanyoyin kasar nan.

Ya kara da cewa rundunar na iya bakin kokarin ta wajen gudanar da bincike domin har yanzu basu san dalilin da zai sa a kaiwa ofishin ta hari ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *