Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shaidawa taron Majalisar koli da ta kunshi tsoffin shugabannin kasa cewa duk da amincewa da bukatun matasa masu bukatar sauyi kan rundunar SARS zanga zanga ta rikide ta zama tarzoma wadda ta kaiga rasa rayuka da asarar dukiyoyi da dama.

Sanarwar da mai bashi shawara kan harkokin yada labarai Femi Adeshina, ya rabawa manema labarai tace shugaban ya shaidawa tsoffin shugabannin irin bukatun matasan da ya amince da su ciki harda rusa rundunar SARS da kuma fara aiwatar da sauye sauye ga rundunar ‘yan Sanda.

Shugaba Buhari ya bayyana damuwa kan yadda tarzomar ta haifar da rasa rayuka da lalata kadarorin gwamnati da na jama’a, yayin da yayi alkawarin cigaba da gabatar da jagoranci na gari.

Sanarwar tace tsoffin shugabannin kasan sun yabawa Buhari kan matakan da ya dauka na dawo da doka da oda wajen jawabin da ya yiwa al’umma da kuma kwantar da hankalin jama’a.

Tsoffin shugabannin sun mika sakon ta’aziyyar su ga mutanen da suak rasa ‘yan uwan su cikin su harad fararen hula da sojoji da kuma yan sanda, yayin da suka jadadda matsayin su na tabbatar da doka da oda da kuma ‘yancin ‘yan kasa, ciki harad zanga zangar lumana.

sun bukaci matasa da su nemi bukatun su ta hanyar tattaunawa da gwamnati, yayin da ita ma gwamnatin aka bukace ta da ta gudanar da taro da su da masu ruwa da tsaki a cikin kasa.

Wadanda suka halarci taron sun kunshi Janar Yakubu Gowon, da Olusegun Obasanjo, da Janar Ibrahim Babangida, da Chief Ernest Shonekan, da Janar Abdusalami Abubakar, da Dr Goodluck Jonathan, da kuma mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da manyan hafsoshin soji da kuma wasu ministoci.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *