Wasu da ake zargin masu zanga-zangar adawa da rundunar Sars ne sun kashe mutane biyu tare da ƙona dukiyoyi a birnin Aba na Jihar Abia.

Lamarin ya faru ne yayin da mutanen ɗauke da adduna da itatuwa suka far wa wata kasuwar kayan gwari, wadda akasari Hausawa ne.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan Sandan jihar, Geoffery Ogbonna, bai yi cikken bayani akan batun ba.

Daga karshe dai gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita a biranen Aba da Umuhia, sai dai matakin bai sa masu zanga-zangar janyewa ba.

Daya daga cikin shugabannin ‘yan arewa mazauna Aba Haladu Imam an far musu ne da misalin ƙarfe 4:30 na yamma.

Haka kuma birnin Fatakwal na jihar Rivers an samu hare-hare duk da dokar hana fita da aka sanya.

Wani mazaunin yankin ya dauki hoton bidiyo na yadda ake dauki ba dadi a tsakanin ‘yan Arewa mazauna yankin da kuma masu zanga-zangar akasari masu fafutukar kafa kasar Biafra.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *