Aƙalla mutane 10 sun mutu sakamakon rikicin da ya biyo bayan zaɓen shugaban ƙasar Guinea.

Ministan tsaron ƙasar ne ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.

A yanzu haka Shugaba Alpha Condé ne ke kan gaba a sakamakon da hukumar zaɓe ta sanar daga mazaɓa 14 cikin 20.

Abokin hamayyarsa Cellou Dalein Diallou ya yi iƙirarin samun nasara, kuma ya zargi Shugaba Conde da murɗe sakkamakon zaɓen.

Sai dai an gudanar da zanga-zanaga da dama tun kafin zaɓen domin nuna adawa da yunƙurin Alpha Conde na sake zama shugaban ƙasa a karo na uku.

Amnesty International ta ce mutane 50 ne suka mutu yayin zanga-zangar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *