Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na 3, ya umurci dukkanin Limamai da su maida hankali a hudubarsu ta Juma’a wajen fadar da al’umma tare da kwantar da hankula kan zanga-zangar adawa da rundunar Sars.

Sultan wanda shine shugaban majalisar koli kan harkokin addinin Musulunci, ya bada umurnin ne a cikin wata sanarwa ta hannun babban jami’in yada labarai na kungiyar Femi Abbas.

Basaraken ya ce zaman lafiya shine hanya daya tilo da idan aka hada da addu’a za a samu ci gaba mai dorewa da kuma shawo kan wasu matsaloli dake ciwa kasa tuwo a kwarya.

Sannan ya yabawa Limaman bisa irin namijin kokari da suka yi musamman wajen kaucewa amfani da kalamai da ka iya tunzura jama’a a lokacin da zanga-zangar ta yi kamari.

Sultan ya yabawa al’ummomin Musulmin Najeriya, kan irin matsayar da suka dauka akan zanga-zangar dake gudana yanzu haka, musamman biyayya ga abin da addini ya tsara.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *