Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce ta fara wani shiri na musamman domin kara horas da jami’anta sabbin dabaru da za su yi amfani dasu wajen yakar ayyukan ta’addanci.

Shugaban rundunar Air Marshal Sadiq Abubakar, ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci jami’an dake samun horon, da kuma wuraren da aka samar na musamman domin bada horon a Bauchi.

Ya ce jami’an hukumar 180 suka samu horo na makwanni 6, a cikin makwanni 13 da suka kwashe suna samun horon na musamman.

Abubakar wanda ya samu wakilcin kwamandan runduna ta musamman dake yaki da  ayyukan ta’addanci a yankin Air Vice Marshal  Charles Ohwo, ya ziyarci mutane da dama.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *