Gwamnatin tarayya ta bukaci hadin kan shugabannin kasashen Afrika wajen sanya ido kan cinikin ma’adanai da da sauran albarkatun kasa ta kan iyakoki ba basi ka’ida ba.

Karamin ministan ma’adanai cinikayya da zuba jari Uchechukwu Ogah, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun jami’in yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar Tine Iulun.

Sannan ya bukaci tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a nahiyar ta yadda za a samar da ci gaba a bangarori da dama da za su samar da ayyuka ga matasa da sauransu.

Ministan ya yabawa hadin kan da gwamnatin kasar Burkina Faso ta ada wajen tabbatar da kykkyawar alaka, a tsakanin kasashe, tare da zuba jari a bangaren kamfanoni masu zaman kansu.

A nasa jawabin ministan ma’adanai na kasar Burkina Faso, Oumarou Idani, ya ce gwamnatin kasar ta maida hankali wajen hakowa tare da sarrafa ma’adanai musamman gwal, domin shine babban hanyar da dake samar mata kudaden shiga.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *