Majalisar wakilai ta koka kan karancin kudi da aka warewa bangaren kimiyya da fasaha a kasafin kudin wannan shekarar da aka gabatar a gabanta.

Shugaban kwamitin kula da harkokin kimiyya da fasa na majalisar Beni Lar, ta bayyana haka a lokacin da ta jagoranci ‘ya’yan kwamitin zuwa ma’aikatar.

Majalisar ta bada tabbaci akan kudurin da take dashi na karawa bangaren kudi a kasafin wanda hakan zai bada damar gudanar da ayyuka yadda ya kamata.

Lar ta ce kaso kasa da daya cikin dari kawai aka warewa ma’aikatar, wanda ba zai kai ta gudanar da wasu karin ayyukan dake gabanta ba.

Ta ce daga daga cikin sirrin da yasa kasashen da suka ci gaba suke amfana da bangarorin shine yadda suke zuba jari sosai, tare da ba bangaren muhimmanci.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *