Ma’aikatar kula da harkokin masana’antu, cinikayya da zuba jari ta ce za ta yi aiki kafada da kafada da wasu hukumomin gwamnati wajen tabbatar da an samar da kudaden gudanarwa a shirin sanin makamar aiki na dalibai.

Ministan masana’antu, kasuwanci da zuba jari Adeniyi Adebayo ya bayyana haka a lokacin da yake magana a wajen taron da asusun dalibai masu sanin makamai aiki ya shirya a Abuja.

Adebayo wanda ya samu wakilcin Daraktan sashen gudanarwa na ma’aikatar Simon Alabi, ya ce shirin na bukatar kudade da za su taimaka wajen gudanarwa, tare da horas da daliban.

Ministan ya ba masu ruwa da tsaki tabbacin cewa duk matsayar da aka cimma za a tura ma’aikatar domin tabbatar da ganin an dauki matakan da suka kamata.

A nata jawabin karamar ministan kula da ma’aikatu, kasuwanci da zuba jari Maryam Katagun, ta yabawa hukumomin shirin, wanda a cewarta asusun ya horas da ‘yan Najeriya akalla dubu dari 5.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *