Gwamnatin jihar Katsina ta amince da sake bude makarantun firaimari da sakandire daga ranar 5 ga watan Oktoban nan da muke ciki.

Kwamishinan ilimi na jihar Badamasi Lawal, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Katsina.

Ya ce daliban za su ci gaba daga inda suka tsaya na kammala zangon karatu na biyu, da ya samu cikas biyo bayan bullar cutar Korona, watanni 6 da suka gabata.

Lawal ya ce ana kyautata zaton kammala zangon karatun na biyu a ranar 23 ga wannan watan kafin daga bisani a fara zangon karatun na 3 daga ranar 26 zuwa 5 ga watan Fabrairun shekara mai zuwa.

Kwamishinan ya ce gwamnati za ta ci gaba da sanya ido domin tabbatar da cewa ana bin dokar bada tazara, sannan za a wajabtawa malaman da daliban sa takunkumin kariya.

Ita ma gwamnatin jihar Kebbi, ta sanar da ranar 4 ga wannan watan a matsayin ranar sake bude makarantu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *