Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana bukatar da take akwai ga gwamnati da kuma ‘yan Najeriya na daukar wasu tsauraran matakai dan samar da ci gaba.

Shugaban ya bayyana hakan ne a cikin sakonsa na murnar zagayowar ranar samun ‘yan cin kai daga kasar Burtaniya.

Ya ce kadarorin da ma’adinai da Najeriya ke da su, sun yi karanci, wanda hakan ya sa gwamnatinsa shiga mawuyacin hali wajen fitar da kasafin kudi.

Shugaban ya kuma zargi tsofaffin shugabannin Najeriya, musamman wadanda ke sukar wasu matakai da gwamnatinsa ke dauka duk da cewa sun san irin barnar da suka yi a lokacinsu.

Akan matakin cire tallafin man futur, shugaban ya ce farashin man fetur a Najeriya na da matukar arha idan aka kwatanta da sauran kasashen duniya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *