Babban sufeta janar na ‘yan sandan Najeriya Mohammad Adamu, ya ba jami’an rundunar umurnin kara maida hankali a rangadi da suke a sassan Najeriya musamman a yanzu da ake ci gaba da murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kai.

Mai magana da yawun rundunar na kasa Frank Mba, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Ya ce shugaban rundunar ‘yan sandan ya bada umurnin ne domin ci gaba da zama a cikin shirin kota kwana na dakile duk wani abu da ka iya tasowa a wani waje.

Sufetan ‘yan sandan ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da shagulgulan su na zagayowar ranar samun ‘yan cin kai cikin walwala ba tare da fargabar komai ba.

Ya ce rundunar ta umurci kwamishinonin ‘yan sanda da sauran mataimakan sufeton ‘yan sanda da su tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin al’umma musamman a wannan lokaci.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *