Majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da daftarin kasafin kudi na naira tiriliyan 13 da milliyan 8 na shekarar 2021. 

Ministar kudi, kasafi da tsare-tsare Zainab Ahmed, ta bayyana haka a lokacin da take zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa jim kadan bayan kammala taron majalisar.

Ta ce anyi hasashen samun naira trilliyan 7 da billiyan 89 a bangaren kudaden shiga, yayin da akwai gibin naira trilliyan 4 da billiyan 48 na kasafin kudin. 

Ministar ta kara da cewa akwai kashi 29 a cikin dari na kasafin kudin da za a kashewa bangaren manyan ayyuka, ta ce an samu kari akan kashi 24 na shekarar nan da muke ciki.

Zainab ta ce zuwa watan Yulin wannan shekarar, kashi 68 cikin dari kawai aka samu hasashen da aka yi, yayin da aka aiwatar da kashi 92 cikin dari na wasu ayyuka. 

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *