Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gaggauta zuba Dala biliyan 15 a wani asusun kasashen duniya domin samarwa da kuma rarraba riga-kafin cutar korona a sassan duniya.

Hadakar Kasashen Duniya mai yaki da cutar Covid-19 karkashin jagorancin Hukumar Lafiya ta Duniya, ta samu kimanin Dala biliyan 3 daga cikin Dala biliyan 38 da ake bukata domin cimma bukatar duniya ta samarwa da kuma rarraba riga-kafin.

Ana dai fatan wannan hadakar na fatar yi wa mutane miliyan 245 magani da kuma gudanar da gwaje-gwaje har guda miliyan 500 nan da shekarar 2021.

Daga cikin manyan alkawuran da aka yi na cika wannan asusun, har da karin tallafin Euro miliyan 100 da shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce za ta bayar duk da cewa a can baya kasarta ta sanar da aniyar bada tallafin Euro miliyan 675.

Ministan Harkokin Wajen Birtaniya, Dominic Raab ya ce, kasarsa da tuni ta yi alkwarin Pam miliyan 250, za ta kashe karin Pam miliyan 250.

Firaministan Sweden Stefan Lofven ya yi alkawarin bada Dala miliyan 10, yayin da takwaransa na Canada, Justin Trudeau ya ce, za su bada Dala miliyan 440.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *