Tawagar kungiyar tarayyar turai a Najeriya ta bukaci ‘yan Najeriya su rika yin abubuwan da za su kawo hadin kai da zaman lafiya, tare da kaucewa bambancin kabilanci, addini da al’ada.

Shugaban tawagar a Najeriya Ketil Karlsen, ya bada wannan shawarar a sakon burnar zagayowar ranar samun ‘yan cin kai shekaru 60 da suka gabata a Abuja.

Ya ce kungiyar na alfahari da ci gaba da kasancewar Najeriya a matsayin kasa dunkulalliya.

A cewarsa hadin kai da Zaman lafiya shine zai haifar da makoma mai kyau ga Najeriya a nan gaba.

Karlsen, ya ce duk da cewa Najeriya na fama da matsaloli, ya zama wajibi a tuna da irin nasarori da ci gaba da Najeriya ta samu a shekaru 60 da suka gabata.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *