Kungiyar gwamnoni ta Najeriya ta ce matukar ba a dauki matakin da ya kamata ba akan ayyukan ta’addancin kungiyar Boko Haram, hakan na iya zama babbar barazana ga Najeriya baki daya.

Shugaban kungiyar, kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci tawagar gwamnonin zuwa jihar Borno domin jajantawa gwamnan jihar.

Daga cikin gwamnonin da suka kai ziyarar akwai gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, sai gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu da na jihar Plateau, Simon Lalong.

Fayemi ya bukaci gwamnan jihar da ya ci gaba da yin taka tsan-tsan musamman a lokutan da yake kai ziyara, duk da a baya gwamnan ya sha cewa ransa a hannun Allah yake don haka baya tsoro.

Shugaban kungiyar ya kuma mika tallafin naira milliyan dari a madadin kungiyar gwamnonin, ga gwamnan jihar ta Borno, domin ci gaba da samarwa wadanda rikicin ta’addanci ya shafa walwala.

A nasa jawabin gwamnan Borno Babagana Zulum, ya sha alwashin ci gaba da yin taka tsantsan a lokacin da yake gudanar da zagaye domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *