Gwamnatin tarayya ta ce an samu nasarar kera na’urar gwajin cutar korona a cikin gida wanda ka iya bada sakamakon gwaji cikin mintuna 40 kacal.

Karamin ministan lafiya Olorunnimbe Mamora ya sanar da haka a wajen taron manema labarai da kwamitin yaki da cutar korona ke shiryawa kullum a Abuja.

Mamora ya ce Cibiyar Bincike da Nazarin magunguna ce ta kera na’urar wanda zai taimakawa Najeriya wajen ci gaba da gwaji ga marasa lafiya.

A baya-bayan nan dai kwamitin ya fara kulle wasu cibiyoyin gwajin cutar korona bayan da ta ke ci gaba da samun raguwar sabbin kamuwa da cutar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *