Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya rantsar da wasu sabbin manyan sakatarori hudu kafin a fara gudanar da taron majalisar ministoci ta intanet a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Sabbin manyan sakatarorin hudu da su ka hada da maza uku da mace daya, sun zama cikon mutane 16 da aka nada cikin watan Yunin bana, wanda daga ciki aka rantsar da mutane 12 sama da wata guda da ya gabata. Manyan sakatarorin kuwa sun hada da Mr James Sule daga jihar Kaduna, da Isma’ila Abubakar daga jihar Kebbi, sai kuma Mrs Ibiene Patricia Roberts daga jihar Rivers da Mr Shehu Aliyu Shinkafi daga jihar Zamfara.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *