Majalisar zartarwar ta kasa ta yi hasashen bunƙasar tattalin arziƙi da kashi uku cikin 100 da kuma hauhawar farashi da kusan kashi 12 cikin 100 a kasafin kuɗi na shekara ta 2021.

Fadar shugaban ƙasa ta ce majalisar zartarwar ta na hasashen Nijeriya za ta riƙa fitar da kowace gangar man fetur a kan dala 40, da kuma samar da gangar mai miliyan 1 da 86 a kowace rana a kasafin kuɗin.

Sakamakon irin illar da annobar korona ta yi wa Nijeriya, tattalin arziƙin ta ya ragu da kashi 6  cikin 100 a watanni shida na farkon shekara ta 2020.

Wannan dai ya na nufin Nijeriya za ta fuskanci matsin tattalin arziƙi a cikin watanni tara na farkon wannan shekarar, inda gwamnatin tarayya ke hasashen cewa tattalin arziƙin Nijeriya zai ƙara raguwa da kusan kashi 9 cikin 100.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *