Gwamnatin tarrayya ta bada umurnin dakatar da shige da fice a duk wasu hanyoyin da za su kai dandalin Eagle square da ke Abuja tun daga tsakar daren Larabar nan, don shirya wa bikin murnar cikar Nijeriya shekaru 60 da samun ‘yancin kai.

Ministan yada labarai da al’adu Lai Muhammad ya sanar da haka, domin tabbatar da tsaron ciki da wajen Dandalin, inda aka tsara yin shagalin bikin a cikin babban birnin tarayya Abuja.

Haka kuma, za a dakatar da shiga Titin Shehu Shagari da Ahmadu Bello, da titunan shige da ficen tashoshin jiragen sama, da duk wasu titunan da ke haduwa da shiga babbar sakateriyar tarayya daidai misalign karfe 2.00 na rana.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *