Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan, ya ce masu zargin gwamnatin shugaba Buhari da rashawa ‘yan adawa ne.

Ahmed Lawan ya bayyana haka ne, a wajen taro na biyu da aka yi a kan yaki da rashawa da hukumar ICPC ta shirya, inda Sanatan ya ce gwamnatin shugaba Buhari ta jajirce wajen yaki da rashawa.

Ya ce, ba zai yi amfani da jita-jita ba, amma ya na so a nuna ma shi ta inda rashawar wannan gwamnatin ta fi na wadda ta gabata.

Ahmad Lawan ya kara da cewa, wannan gwamnatin ba ta taba kama wani da laifin rashawa ta bar shi haka nan ba tare da an hukunta shi ba, amma idan mutum dan adawa ne zai iya fadin komai.

Ya ce ba don ya na tare da wannan gwamnatin ba, zai iya cewa abubuwa 3 wannan gwamnatin ta fi maida hankali, wadanda su ka hada da yaki da rashawa da yaki da ta’addanci sai kuma tabbatar da tsaro da kuma bunkasa tattalin arziki.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *