Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa John Oyegun, ya ce tun farko mulkin shugaba Muhammadu Buhari bai zo  cikin sa’a ba.

Yayin zantawa da manema labarai a gidan sa da ke Benin, Oyegun ya ce ba don salon mulkin ba, da Nijeriya ba ta samu ci-gaban da ta samu a yau ba.

Da ya ke tsokaci a kan manyan kalubalen da su ka addabi kasar nan, Oyegun ya ce wadanda ke mulki a yanzu ba su yin kokarin da ya dace kuma hakan ya sa ‘yan Nijeriya su ka karaya.

Ya ce ‘yan Nijeriya sun a fama da yunwa, kuma tattalin arziki baya habbaka baya ga rashin aikin yi da ta’addanci da sauran su.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *