Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce akwai batutuwan da ake bukatar warwarewa game da shirin sojin Mali na mika mulki ga farar hula kafin kungiyar Ecowas ta cire takunkumin da ta sanya wa kasar.

Ecowas dai ta sanya wa Mali takunkumin ne, bayan juyin mulkin da sojoji su ka yi wa Shugaba Ibrahim Boubacar Keïta a watan da ya gabata.

Daya daga cikin sharudan janye wa kasar takunkumi shi ne nada shugaba da firayin minista farar hula.

Duk da ya ke sojojin sun cika sharadin, shugaban su Kanar Assimi Goita ya na ci-gaba da zama a matsayin mataimakin shugaban kasa, lamari da har yanzu bai gamsar da kungiyar Ecowas ba.

Ofishin Shugaba Buhari ya fitar da sanarwar cewa, watakila shugabannin kasashen Yammacin Afirka za su sake ganawa domin tattaunawa a kan rikicin siyasar Mali, bayan ya gana da wakilin Ecowas kuma tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *