Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya yi gargadin cewa Nijeriya ta na fuskantar rugujewa, inda ya bukaci al’umma su cigaba da addu’a da kuma jajircewa wajen ganin ta dore.

Osinbajo ya bayyana haka ne, yayin da yak e jawabi a wata Mujami’a ta kasa da ke Abuja, dangane da bikin cika shekaru 60 da samun ’yancin kan Nijeriya, inda ya ce har yanzu akwai fata mai kyau duk da ya ke wani sashen Nijeriya ya fara tsagewa.

Ya ce Nijeriya ta na bukatar wani manzo a yau, domin tunkarar dimbin matsalolin da su ka addabe ta duk da tsananin adawar da zai gamu da ita.

Yayin da ya ke bayyana fatan ganin cika shekaru 60 zai bude wani sabon babi a Nijeriya, Osinbajo ya ce babu wata kungiya da ke shirye wajen tunkarar matsalolin da su ka wuce na addinai.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *