Majalisar dattawa ta koma bakin aiki, bayan hutun shekara da ta je na tsawon sama da watanni biyu.

A zaman ta na ranar 23 ga watan Yuli, majalisar ta sa 15 ga watan Satumba a matsayin ranar da za ta koma, amma sai mukaddashin magatakardar majalisar ya sanar da dage dawowar zuwa ranar 29 ga watan Satumba.

Majalisar dai ta fara ne da gudanar da wata ganawar sirri a karkashinjagorancin Sanata Ahmad Lawan, inda su ka tsara muhimman abubuwa da dama wadanda ‘yan majalisar za su yi nazari a kan su.

Daya daga cikin abubuwan kuwa sun hada da dokar man fetur, wadda Sanata Lawan ya ce za a karanta wata wasika daga Shugaba Muhammadu Buhari game da hakan, sai kuma rahoton kwamitin kasafin kudin da za a kashe na shekara ta 2021 da 2023.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *