Wata babbar kotu da ke zama a Kaduna, ta bada umurnin a cigaba da shari’ar da ke gaban ta a kan jagoran mabiya Shi’a Sheik Ibrahim Zakzaky.

Sheikh Zakzaky da matar sa Zeenatu dais u na tsare tun a shekara ta 2015, bayan mutuwar mabiyan akidar Shi’a sama da 300 a wata arangama da jami’an tsaro a garin Zaria.

Sojoji sun ce sun bude wa mabiyan wuta ne a matsayin martani bayan sun yi kokarin kai wa ayarin motocin babban hafsan sojin kasar hari.

A shekara ta 2019 ne aka haramta kungiyar bayan shafe tsawon watanni na zanga-zanga da rikici da jami’an tsaro.

Lauyan Zakzaky Femi Falana, ya bukaci kotun ta yi watsi da tuhumar da ake yi wa El-Zakzakky, sai dai alkalin kotun ya ce hakan ba mai yiwuwa ba ne, domin bai gama sauraren gundarin karar da aka shigar ba balantana ya yanke hukunci. Yanzu haka dai Alkalin kotun ya bayyana Nuwamba a matsayin watan ci-gaba da sauraren shari’ar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *