Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa, ta ce gayyaci kamfanoni domin kera na’urar da ta dace da nufin komawa jefa kuri’a nan gaba ta hanyar na’ura mai kwakwalwa.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmud Yakubu, ya ce hukumar ta gayyaci masu kera na’urorin kada kuri’a daga sassan duniya, domin gwada yadda za a yi aiki da fasahar a Nijeriya domin zaben na’urar da ta fi inganci.

Farfesa Yakubu, ya ce duk kamfanoni 40 da a ka gayyata za su gwada fasahar su domin tantance ko na’urar za ta kara ingancin zabe a Nijeriya.

Hukumar zaben, ta ce ta bullo da tsarin yanar gizo, mutane za su iya ganin sakamakon zaben rumfunan zabe a ranar da a ka kada kuri’a, sai dai har yanzu ba a tabbatar da dokar da za ta ba hukumar zaben damar aiwatar da wannan tsarin ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *