Gwamnatin tarayya ta na shirin sayar da kamfanin man fetur, tare da sake fasalin rabon kudaden da ake samu daga man fetur, kamar yadda sabuwar dokar da shugaba Buhari ya gabatar wa Majalisar dokoki ta kun sa.

Daftarin dokar ya na kunshe ne da yadda za a sake dokokin da su ka shafi hakar mai da iskar gas sakamakon matsalar da ake samu wajen raba arzikin kasa.

Dokar ta kunshi bada damar kafa wani sabon kamfani da zai ba ministan kudi da na mai damar maida kadarorin kamfanin NNPC zuwa wurin, yayin da gwamnati za ta biya hannayen jarin kamfanin, wanda zai rika gudanar da aikin sa a matsayin kamfanin kasuwanci da ba ruwan shi da kudaden hukuma.

Ana sa ran Majalisa ta kuma yi wa dokar man gyara dangane da abin  da ya shafi yadda ake hako mai a cikin teku, da kuma rage kudaden da kamfanonin hakar man ke ba gwamnati a wuraren da su ke hako man da bai kai ganga dubu 15 a kowacce rana daga kashi 10 zuwa kashi 7 da rabi ba.

Sabuwar dokar, ta kuma bada damar soke hukumar daidaita farashin mai da kuma kirkiro sabuwar hukumar da za ta maye gurbin hukumar  kayyade farashin mai domin rage wasu ayyukan da hukumar DPR ke yi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *