An rasa ran mutum daya a garin Jibiya, yayin da al’ummomin yankin su ka shirya zanga-zanga sakamakon matsalar rashin tsaro da ke addabar su a jihar Katsina.

Al’ummar Jibiya dai sun yi zanga-zangar ne domin nuna rashin jin dadin abin da ke faruwa na yawaitar kashe-kashe, inda sakamakon haka aka harbe wani mutumi har Lahira.

Rahotanni sun ce, jami’an tsaro sun kama mutane akalla 43, kuma ana zargin ‘yan sandan da aka tura domin hana zanga-zangar ne su ka harbi mutumin.

Wani mutum da ya fito daga kauyen Daddara mai suna Falalu Abba, ya ce dole ce ta sa talakawan yankin su ka fita zanga-zanga domin nuna bacin ran su, domin tsawon kwanaki 39 kenan a jere kullum sai an kai masu hari, sannan idan aka kira jami’an tsaro sai su ki zuwa, don haka ya ce mutane sun gaji shi ya sa su ka dauki doka a hannun su.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *