Wata babbar kotun tarayya ta umurci Sanata mai wakiltar mazabar Adamawa ta arewa Elisha Abbo, ya biya Naira miliyan 50 a matsayin diyya ga Osimibibra Warmate a kan cin zarafin ta da ya yi.

An dai gurfanar da Sanata Abbo a gaban wata kotun majistare da ke Zuba, bisa tuhumar sa da cin zarafin Warmate a wani shagon saida da kayan batsa a Abuja.

Duk da hujjar bidiyon lamarin da aka gabatar, alkalin kotun Abdullahi Ilelah ya kori shari’ar, sai dai Warmate ta shigar da karar neman ‘yanci a gaban babbar kotun tarayya.

Da ya ke zartar da hukunci, alkalin ya kama Sanata Abbo da laifi, sannan ya umurce shi ya biya mai tarar naira miliyan 50.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *