Daukacin Jihohin Nijeriya 36 sun garzaya kotun koli, domin kalubalantar wata dokar shugaban kasa mai cikakken iko.

Gwamnonin dai za su kalublanci shugaba Muhammadu Buhari a gaban kuliya a kan batun yadda za a rika tafiyar da harkokin kotu a Nijerya.

Wata majiya ta ce, gwamnonin sun gabatar da karar ne a gaban kotun koli ta Nijeriya ta hannun kwamishinonin shari’ar su.

Jihohin Nijeriya dai su na bukatar Alkalin ya yi watsi da dokar  ta shugaban kasa Buhari, domin a cewar su ta  ci karo da kundin tsarin mulki da dokar kasa.

Ministan shari’a Abubakar Malami ne kadai wanda karar ta ambata domin ya kare gwamnati, yayin da manyan lauyoyi tara su ka tsaya wa gwamnonin a karkashin jagorancin tsohon shugaban kungiyar Augustine Alegeh.

Gwamnonin dai sun koka da yadda aka yi amfani da dokar wajen dora wa jihohin alhakin kula da albashi da kudin ayyukan wadannan kotunan.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *