Kungiyar ‘yan ta’addan IS, ta dauki alhakin harin da aka kai wa tawagar gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum a garin Baga.

Jami’an tsaro da dama dai sun rasa rayukan su, yayin da wasu su ka jikkata a harin da ‘yan ta’addan su ka kai.

Tuni dai Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da harin.

Shugaba Buhari, ya ce harin maƙarƙashiya ne ga shirin da ake yi na ganin mutanen da rikici ya ɗaiɗaita sun koma gidajen su.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *