Mai Shari’a Ayo Salami, ya ce ya yi nadamar karbar shugabancin kwamitin shugaban kasa na binciken tsohon shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu.

Ayo Salami ya bayyana haka ne, lokacin da ya ke sauraren masu kare Ibrahim Magu a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

‘Yan jarida ba su samu damar halartar zaman da ake yi ba, don haka su ka dogara da wasu Lauyoyi wajen samun bayanan zaman.

Rahotanni sun ce ana samun labarin binciken ne daga lauyoyi da shaidun da su ka halarci zaman, bayan kiran a fadada masu zuwa zaman ya faskara.

Wasu Lauyoyi biyu da su ka tsaya wa Ibrahim Magu da su ka halarci zaman a mako jiya, sun ce Salami ya na nadamar karbar wannan bincike.

Tosin Ojaoma da Zainab Abiola, sun ce Ayo Salami ya fada masu kafin a soma zama cewa ya yi da-na-sanin amincewa da karbar shugabancin kwamitin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *