Rundunar ‘yan sanda ta kama mutum 12 sakamakon zargin su da taimakawa wurin satar amsa yayin zana jarrabawar WAEC da aka kammala a ‘yan kwanakin nan.

Kama mutanen na zuwa ne bayan dawo da ƙawance na musamman da ke tsakanin hukumar shirya jarrabawar ta WAEC da kuma ‘yan sandan Najeriyar.

Binciken da rundunar ‘yan sandan Najeriyar ta yi ta gano cewa waɗanda ake zargin, sun yi amfani da matsayin su na masu sa ido kan jarrabawa wajen taimakawa domin satar amsa.

Babban sifeton ‘yan sandan Najeriyar ya yi kira ga iyayen yara da ɗalibai da masu ruwa da tsaki da ke shirya jarrabawa da su bayar da haɗin kai wurin kawo ƙarshen satar amsa a jarrabawar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *